Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi A Kasar Belgium Sun Bayyana Sunan Wanda Ya Kai Hari Tashar Jirgin Kasa


Fashewa A Tashar Belgium
Fashewa A Tashar Belgium

An bayyana wanda ya kai hari a tasha jirgin kasa a birnin Brussel da ke Belgium dan kasar Morocco ne wanda ba'a taba samun sa da wani aikin ta'addanci ba

Hukumomi a Belgium sun ce mutumin da aka kashe a ranar Talatar da ta gabata yayin wani harin ta’addanci da bai yi nasara ba a tashar jirgin kasa dake birnin Brussels, wani dan kasar Morocco ne mai shekaru 36, wanda ba a taba samunsa da wani aikin ta’addanci ba.

Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi, kakakin ofishin gwamnatin tarayya dake shigar da kara, Eric Van der Sypt, ya bayyana sunan mutumin da harrufan farkon sunayensa ne kawai a matsayin O.Z. Ya kuma kara da cewa an binciki gidan mutumin a daren jiya.

Shi dai wannan harin da aka dakile, an yi yunkurin kai shi ne a tashar jirgin kasa dake tsakiyar birnin Brussels, inda maharin ya tunkari wani taron fasinjoji, ya yi kuwwa ya kuma dana wani dan karamin abin fashewa a cikin akwatinsa.
Daga nan kuma a cewar jami’an tsaron, mutumin ya zura da gudu ya sauka kasa, ya yi kan wani ma’aikacin tashar jirgin, inda a nan akwatin ya fashe.
Sai dai bayanai sun nuna cewa babu wanda ya ji rauni daga harin, wanda ya auku da misalin karfe tara na dare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG