Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi a Najeriya suna so su ci gaba da tsare Bankole har zuwa lokacin da za a gurfanar da shi gaban kotu


Jami'an tsaro a Najeriya

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya tana so ta ci gaba da tsare tsohon kakakin majalisar dokokin kasar har lokacin da za a gurfanar da shi gaban kotu domin amsa tuhumar cin hanci da rashawa da ake yi mashi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya tana so ta ci gaba da tsare tsohon kakakin majalisar dokokin kasar har lokacin da za a gurfanar da shi gaban kotu domin amsa tuhumar cin hanci da rashawa da ake yi mashi. Ana tuhumar Dimeji Bankole da aikata laifuka dabam dabam har 16 na rubda ciki da kudin gwamnati da aka kiyasta a kan dala miliyan sittin. Ya bayyana gaban kotu yau jumma’a domin neman beli, za a kuma ci gaba da tsare shi har zuwa ranar Litinin lokacin da za a ci gaba da sauraron bayanan lauyoyi. Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta lashi takobin kalubalantar duk wani yunkurin bada belinshi sabili da bisa ga cewarta, a fili yake Bankole bashi da niyar bayyana gaban kotu domin sauraron karar bisa radin kansa. Ranar Lahadi hukumomin Najeriya suka kama Bankole bayan sun shafe sa’oi hudu ana ja in ja a gidanshi dake Abuja. Ya musanta aikata laifukan da ake zarginshi da aikatawa lokacin da ya bayyana gaban kotun ranar Laraba. Masu shigar da kara sun ce an hada baki da Bankole, aka kara kudin nau’rar computer da printer da kuma akwatunan talabijin. Ana kuma zarginshi da coge a neman kwangilar sayen motocin kawa. Sabon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi alkawarin shawo kan matsalar cin hanci da rashawa da aka shafe shekara da shekaru ana fama da shi a kasar.

XS
SM
MD
LG