Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Da Shugabannin Addini A Nijar Sun Yi Allah Wadai Da Harin ChristChurch


Dalibai suna zaman makoki a bakin massalain Christchurch, New Zealand
Dalibai suna zaman makoki a bakin massalain Christchurch, New Zealand

Hukumomin da shuwagabanin addinai a jamhuriyar Nijer sun bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen nuna juyayin kisan musulmi a kasar New Zeland kimanin 50, lamarin da shugaba Mahamadou Issouhou yace alama ce dake nuna bukatar a yaki ta’addanci a kowane mataki.

Koda yake ba shine karon farko da harin ta’addanci ke rutsawa da jama’a a wuraren ibada ba, a wannan lokaci na tabarbarewar al’amuran tsaro, harin na masallatan kasar New Zeland wani abu ne da ake kallonsa tamkar wani abin ba za ta.

A cikin hirarsa da Sashen Hausa, Reverend Sabo Batshiri na majami’ar da ake kira EGLISE AD a nan yamai yace ya kamata duk lokacin da aka fuskanci matsala irin wannan a tashi tsaye baki daya ko da wanene ya shafa. Yace akwai bukatar duniya tayi magana da baki daya a tsautawa masu irin wannan aikin da ya ce ko da menene tunanin mai aikata irin wannan tashin hankali, babban laifi ne.

A nashi bayanin, Limamin masallacin majalisar dokokin Nijer Malan Haja Alalo na kallon kisan na masallatan CHRISTCHURCH tamkar wata jarabta mai dauke da abubuwan ishara ga musulmi.

Shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou dake bayyana ra’ayinsa akan harin na new zeland ya rubuta a shafinsa na tweeter cewa, « ina jajantawa al’umar Nouvelle Zeland da iyallan wadanda wannan al’amari ya rutsa da su » sannan ya ci gaba da cewa, « kisan gillar na Chirstchurch wani abin takaici ne dake kara tunatar da duniya cewa ta’addanci wani abu da ba shi da iyaka wanda kuma da ya kamata a yake shi a kowane mataki. »

Saurari cikakken rahoton Souley Mummuni Barma

Tsokaci kan harin Christchurch-2:43"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG