Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Cigaba Da Tsare Dan Rajin Dimokradiya Jimmy Lai a Hong Kong


Hukumomi sun ci gaba da tsare Jimmy Lai, wani hamshakin dan kasuwa mai harkokin sadarwa kuma dan rajin dimokaradiya a Hong Kongbayan da babbar kotun yanki ta hana bada belinshi yayin da ya bayyana gaban ta yau Talata. 

An kama Lai mai shekaru 73 a duniya ne a ranar 3 ga watan Disamba kana ya kwashe makwanni uku a tsare kafin aka bada belin shi kan dala miliyan guda da dubu 200. Masu shigar da kara sun daukaka kara a kan hukunci beli da aka baiwa Lai, suna ikirarin hukunci da karamar kotun ta yanke na cike da kura kurai.

Kotun daukaka karar ta amince da bukatar masu shigar da karar a hukuncin da ta yi, tana ishara da dokar tsaron kasa dake hana bada beli ga mutanen da ake zargin su da aikata laifi ko kare laifi, har sai in alkali ya samu isassun shaida da zai tabbatar da wanda ake zargi da aikata laifin ko kare laifi ba zai ci gaba da aikata ayyuka masu barazana ga tsaron kasa ba.

Da farko an zargi mai kamfanin sadarwa na Next Digit ne da laifin damfara, inda masu shigar da kara ke tuhumarsa da sabawa sharudan inda kamfanin ke aiki.

Da farko ana zargin Lai da aikata laifin hadin baki da wata kasar waje, karkashin sabuwar dokar tsaron kasa.

XS
SM
MD
LG