Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Gano Mutum Da Ya Kashe Mutane Tare Da Raunata Wasu A Jihar Florida


Hukumomi a Jacksonville, jihar Florida dake nan Amurka, sun ce wani mutum dauke da bindiga ya kashe mutane biyu kuma ya raunata wasu mutane tara daga bisani kuma ya kashe kansa a wani wurin da aka shirya wassan bidiyo ranar jiya Lahadi.

Harin ya auku ne cikin wani gidan cin abinci a Jacksonville landing, wani fitaccen wurin shakatawa dake da shaguna da wuraren cin abinci a cikin garin birnin.

Shugaban yan sanda Mike Williams ya ce a lokacin da aka yi harbin akwai mutane dayawa a gidan cin abincin Pizza da suka dauki nauyin gasar bidiyon NFL 19.

Williams yace masu bincike na cigaba da aiki don gano makasudin harin da aka kai.

Kawo yanzu dai, yace masu bincike sun yi amanna da cewa, mutum da ya kai harbin shi kadai, dan shekaru 24 ne mai suna David Katz daga birnin Baltimore a jihar Maryland, kuma yayi amfani da bindigan hannu ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG