Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Borno Sun Tabbatarda Gano Dalibai Ashirin


Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.
Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

A wani yunkuri na kawar da rudani bisa ga ikirarin da aka ce sojoji sun yi dangane da daliban da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace a Chibok, hukumomin jihar Borno sun jaddada cewa kawo yanzu dalibai ashirin ne kawai aka gano.

Yanzu hukumomin jihar Borno sun tabbatarda gano dalibai ashirin cikin wadanda aka sace a makarantar 'yan mata dake garin Chibok, kuma tuni aka hadasu da iyayensu.

Kwamishanan ilimi na jihar Musa Inuwa Kubo shi ya tabbatar wa Muryar Amurka hakan. Kwamishanan ya tabbatar da hakan bayan ya kai ziyarar gani da idanunsa zuwa garin Chibok inda lamarin ya faru. Amma yace ba zai iya tabbatar ko karyata sanarwar da sojoji suka fitar a Abuja ba. Yace mai yiwuwa sun samu kubutar da daliban ne amma su a jihar Borno basu da wannan tabbacin.

Shekaranjiya ne sojoji suka fitar da sanarwa cewa sun kubutar da yawancin yaran saura guda takwas kawai. A kan wannan ikirarin na sojoji kwamisahanan yace baya son su samu sabani da juna. Yace tana yiwuwa daliban na wurin su sojoji. Yace shi da jama'ar Chibok da shugabar makarantar da iyayensu suna nan suna jira sojoji su kawo masu daliban da suka kubutar.

Daya daga cikin iyayen dake garin Chibok yace ba gaskiya ba ne cewa an kubutar da yawancin yaran. Yace maimakon hakan 'yan gora da wasu mafarauta sun kama hanyar dajin da 'yan Boko Haram suka kafa sansani.

Ga rahoton Haruna Dada Biu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG