Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Jihar Mississippi Na Neman Wadanda Suka Cinna Wuta A Wani Coci


Cocin da aka cinnawa wuta a garin Greenville, Mississippi

Hukumomin dake kula da dokokin Amurka sun kaddamar da wani binciken akan kona wani coci da aka yi a kudancin jihar Mississippi kuma daga baya aka kewayeshi da rubuce rubuncen dake cewa a jefa wa Donald Trump kuri’a.

Cocin wanda tsohon coci ne, domin ko yakai kimanin shekaru 111 na yan darikar Baptist nena Hopewell Missionary Baptist Greenvilean kone shi a yammacin ranar Talata.

Magajin garin Errick Simmons yace wannan ya nuna a sararikiyayya ce a fili aka nuna domin baiga dalilin da zaisa a hada batun addini da siyasa ba alhali kuwa kowa nada ‘yancin yin irin addinin da yake sha’awar yi. Yace an yi haka ne domin kawai a musgunawa jama’a.

Magajin garin yace hukumar FBI, da hukumar binciken manyan laifuka ta Mississippi suna taimakawa wajen gudanar da wannan binciken.

Shi dai wannan birnin dake da yawan mutane har dubu 33 yana kusa da bakin iyakar Arkansas ne wadda kashi 78 daga cikin su bakaken Amurkawa ne, kamar yadda kidayar jama’a ta baya-bayan nan ta nuna, cewa kasahi 71 na jama’ar wurin bakake ne.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG