Accessibility links

Hukumomin Najeriya Sun Hana Jirgin Amaechi Tashi


Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi

Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da Sanata Haruna Goje da wasu sun sauka Kano sun mika gaisuwar ta'aziya da taya sabon sarkin Kano murna amma mahukuntan Najeriya basu bar jirgin da ya kawosu tashi ba wai sabili da matakan tsaro.

Biyo bayan da suka gama kai gaisuwar ta'aziya da yiwa sabon sarkin Kano murna mahukuntan Najeriya sun hana jirgin da ya kawo gwamna Amaechi da wadanda suka rufa masa baya tashi.

Sanata Haruna Goje daya daga cikin mutanen dake cikin jirgin da gwamna Amaechi yace bayan sun yiwa maimartaba sarkin Kano ta'aziya sai Daga suka tashi zuwa Abuja amma suka samu ana ruwa kamar da bakin kwarya sai matukin jirgin yace su koma Kano idan ruwan ya dauke su koma Abuja. Minti ashirin da saukarsu Kano aka ce ruwa ya dauke a Abuja sai suka yi shirin tashi. Dama can basu sauka daga jirgin ba, wato gwamna Amaechi da shi Goje da tsohon gwamnan Kwara Sanata Shaba Lafiaji da kuma Alhaji Kawu Baraje.

Suna gaf da tashi matukin jirgin ya fada masu an hanasu tashi. Wai kwamandan sojoji na tashar yace kada kowane jirgi ya tashi ko ya sauka idan ba na 'yan kasuwa ba. Gwamna Amaechi ya bugawa gwamnan Kano ya sanardashi halin da suke ciki shi kuma ya bugawa kwamandan amma abun ya gagara. Kamar da wasa sai aka rufe filin saukar jirgin saman Kano. Dole suka fita daga jirgin suka nemi mota da ta kaisu Abuja.

Babu wani bayani da aka yi masu akan dalilin hanasu tashi. Cikin tsakar dare suka tafi Abuja. Sun isa Abujan wajejen karfe biyun dare.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
XS
SM
MD
LG