Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin New York Sun Rage Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Gobarar Bronx


Lokacin da ma'aikatan kashe gobara suke kokarin shawo kan wutar ta Bronx

Kididdiga ta nuna cewa, kimanin mutum 44 ne suka ji rauni inda 13 daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

Wuni guda bayan mummunan gobarar da ta tashi a gundumar Bronx a birnin New York da ke Amurka, hukumomi sun ce mutum 17 suka mutu a cikin wannan gobara ba 19 ba kamar yadda alkalumman fari suka bayyana.

Wannan adadi da hukumomin suka fitar ya biyo bayan zagawa da hukumomin suka yi a asibitoci da aka kai wadanda gobara ta rutsa da su, kamar yadda babban kwamishinan hukumar kwana-kwana ta birnin New York Daniel Nigro ya fadawa manema labarai inda ya kara da cewa injin din dumama daki ne ya yi sanadiyar gobara.

Asibitotci a birnin New York suna nan suna aiki gadan-gadan domin ceto gomman mutane da suke cikin hali na mutu-kwakwai-rai-kwakwai da suka shaki hayaki da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 17.

Ba a riga dai an bayyana sunaye mutanen da suka mutu ba, amma hukumomi sun ce yaran da suka mutu sun hada da mai shekaru 4 da mai 5 da mai 6 da yaran mata biyu masu shekar sha daya-daya da kuma wani yaro mai shekara 12 kana akwai daya da ba a kammala tantancesa ba.

Kimanin jami’an kashe gobara 200 ne suka yi kokarin kawar da wutar da ta tashi a hawa na uku a cikin bene mai hawa 19 dake unguwar Tremont a Bronx da hantsin ranar Lahadi.

Shugaban hukumar Kwana kwana a birnin New York ya ce hayaki da ya turnuke a cikin ginin ne ya yi sanadiyar mutuwar mutanen.

Nigro ya ce an kai gawarwakin asibitoci bakwai na birnin wanda ya yi bayani a kan sauya adadin wadanda suka mutu daga 19 zuwa 17 saboda an kirga wasu sau biyu biyu.

Kididdiga ta nuna cewa, kimanin mutum 44 ne suka ji rauni, amma 13 a ciki raunin nasu sun yi tsanani, lamarin da ka iya sanadiyar mutuwar su.

XS
SM
MD
LG