Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Cafke Wasu Tsoffin Shugabannin Hukumar Shige Da Fice Akan Cin Hanci Da Rashawa


Bazoum Mohamed da wasu shugabannin kasar Nijar
Bazoum Mohamed da wasu shugabannin kasar Nijar

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun cafke wasu tsofaffin shugabannin hukumar shigi da ficin kaya a ci gaba da binciken da hukumar yaki da cin hanci ta kaddamar kan wata badakalar da ta shafi dubban miliyon cfa wace ake hasashen za ta iya rutsawa da dimbin jami’an Douane, wato kwastam.

NIAMEY, NIGER - To sai dai kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawar sun bayyana fatan ganin an yi aiki da doka don ganin an hukunta masu laifi an kuma wanke wadanda ba su da hannu a ciki.

Binciken da hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA ta gudanar a ma’aikatar Douane ne ya bada damar bankado wata almundahanar da a ke zargin an tafka a zamanin da General na Jandarmomi Amadou Halidou da kanal Oumarou Amadou mai lakanin Petitot suka shugabanci hukumar ta DGD lamarin da ya sa aka kulle su a kurkuku a ci gaba da neman haske akan wannan cuwa cuwa da ta shafi million 16000 zuwa 18000 na cfa.

Jami’in fafutika ta yanar gizo Bana Ibrahim na daga cikin masu bin diddigin wannan labari.

Wasu majiyoyin hukumomi sun ayyana cewa dimbin jami’an Douane ne ake hasashen an hada baki da su wajen karkata akalar wadannan kudade saboda haka akwai yiyuwar wannan yunkuri ya rutsa da ma’aikata kusan 100.

Dalilin haka ne shugaban reshen kungiyar yaki da cin hanci Transparency International a Nijar, Malan Maman Wada ke gargadin mahukunta akan bukatar gudanar da lamura a karkashin abubuwan da doka ta yi tanadi ta yadda za a yi abin cikin yanayin adalci.

Shugabannin kungiyar jam’ian Douane ta SNAD da muka tuntuba sun sanar cewa suna gudanar da taron hadin gwiwa da shugabannin hukumar DGD da jami’an ma’aikatar ministan kudi saboda haka za su shaida mana bayan kammala wannan zama amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba su wani bayani daga gurunsu ba.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Hukumomin Nijar Sun Cafke Wasu Tsoffin Shugabannin Hukumar Shiga Da Fice Akan Cin Hanci Da Rashawa .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG