Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Saudiyya Sun Karyata Rade-radin Shirin Saukar Sarki Salman daga Sarauta


Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud

Hukumomin Saudiyya sun karyata rahotannin da ke cewa Sarki Salman bin Abdul’aziz al Saud na shirin sauka daga gadon sarauta ya baiwa dansa Yarima Muhammad bin Salman.

“Ko alama babu yiwuwar Sarkin zai sauka ya saka wani,” abin da wani babban jami’in Saudiyya ya gaya ma kafar labarai ta Bloomberg kenan bisa sharadin sakaya sunansa, ya na mai nuni da yadda Sarakunan Saudiyya kan cigaba da zama bisa gadon sarauta ko da kuwa rashin lafiya ya hana su gudanar da ayyukansu.

Rade-radin yiwuwar Sarki Salman ya sauka sun fara bayyana a makon jiya bayan da wata tashar talabijin ta Iran mai suna Press TV, ta ce kwanan nan Yariman zai hau gadon sarauta saboda Sarki Salman zai yanke shawara kwanan nan.

Jami’in na Saudiyya ya gaya ma kafar ta Bloomberg cewa Sarki Salman, dan shekaru 81 da haihuwa na da cikakken lafiya ta fuskar jiki da kuma kwakwalwa.

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG