Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Saudiyya Zasu Tantance Hadisan Manzon Allah (SAW)


Sarki Salman na Saudiyya

Makon jiya ne kasar Saudiyya ta ce zata tantance Hadisan Manzon Allah (SAW) a Birnin Macca domin kawar da yadda ake rudan matasa suna shiga ta’addanci da sunan addinin, matakin da malaman Islama a jihar Najeriya suka ce zai taimaka matuka

Malaman addinin Islama a Najeriya sun ce matakin da kasar Saudiyya ta dauka na tantance Hadisan Manzon Allah (SAW) zai taimaka matuka wajen shawo kan matasan musulmai dake hankoron shiga kungiyoyin ta’addanci.

Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban kungiyar IZALA a Najeriya, ya ce baicin shawo kan masu tunanen shiga ta’addanci, matakin zai taimakawa dalibai masu neman ilmi da zasu karu da wasu hanyoyi da dama. Ya bayyana cewa tantance Hadisan ba wai za’a canza wani abu ba ko a kawo sassauci kuma ba domin Amurka za’a ba. Ya ce sai an samu malamai na kirki da zasu ba da fatawa da zai taimakawa mutane.

Shaikh Abdullahi Lau shugaban kungiyar IZALA
Shaikh Abdullahi Lau shugaban kungiyar IZALA

Shi ma jigon darikar Tijjaniya a jihar Neja, Imam Shehu Rimaye, bayan ya nuna gamsuwa da matakin na Saudiyya, ya ce babu wani hadishin da ya amince da a je a yi aikin ta’addanci ko kuma ya koyas da ta’addanci. Ya ce akwai bukatar gyara na gaske.

Mustapha Nasiru Batsari na da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG