Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukuncin Kisa Ga Duk Wanda Yayi Sama Da Fadi Da Dukiyar Kasa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari .

Da farko sai anyi tankade da rairaya a fanin sharia.

Yau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayi juyayi da nuna bakin cikinsa akan yadda wadansu shuwagabanin suke amfani da ammanar da kasa ta basu wurin yin handama da babakere da kuma tara dukiyar data zarce hankali wanda zuri’arsu bazata gama kashe dukiyar ba.

Muhammadu Buhari dai yana wannan jawabin ne a wani taro da aka shirya domin jinjinawa gidauniyar tallafawa jama’a na Osagwe Ayim Osagwe, inda shugaban kasar ya ce babu shakka sace sacen da wasu shugabanin suka yi a Najeriya, ya nuna a zahiri cewa babu kamata adalci da kuma tsoron cin amana ganin irin barna da tabargazar da akayi akan dukiyar kasa.

Daya daga ciki shuwagabanin kungiyar ceton kasa ta Najeriya, Hajiya Naja’antu Muhammad, ta ce ta inda za’a iya magance irin wannan ta’asa da ake tafkawa Najeriya, shine ta hanyar hukunci.

Ta kara da cewa ita da so samu ne na farko sai anyi tankade da rairaya a fannin sharia, dan sau dayawa sa’a kama mutun dumudumu amma za’a samu alkalai a raba kudin dasu su saki mutun, yakamata mutanen kasar nan mu tashi a sa hukuncin kisa kamar yadda China take duk wanda aka sameshi da laifin irin wannan ta’asar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00

XS
SM
MD
LG