Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukuncin kisa da Bangladesh ta yiwa shugaban jam'iyyar Islama ya jawo cecekuce


Kotun kolin Bangladesh da ya yankewa Motiur Rahman Nizami hukuncin kisa

Ana samun musayar ra’ayoyi daga ciki da wajen kasar Bangladesh, game da zartar da hukuncin kisan da aka yi jiya Laraba akan shugaban wata jam’iyyar Islama a kasar, bisa zarginsa aikata laifuffuka a lokacin yakin shekarar 1971.

Yakin da suka yi na ballewa daga kasar Pakistan don neman ‘yancin kai. Masu fafutukar da ke goyon bayan hukunta laifuffukan yakin Bangladesh, da kuma ‘yan uwan wadanda aka kashe a yakin sun goyi bayan wannan hukuncin kisa.

Wanda aka yankewa hukunci Motiur Rahman Nizami, wanda shine shugaban jam’iyyar musulunci mafi girma ta Jamaat-el-Islami. Wanda suka bayyana shi a matsayin wanda ya kitsa kisan malamai da wasu jama’a da fyade da azabtar al’umma a yakin.

Amma masu rajin kare ‘yancin bil’adama sunce, an rataye Nizami ne biyo bayan wata shari’a mai rauni a karkashin kotun hukunta laifuffukan yakin kasa da kasa ta kasar, inda ta yanke masa hukuncin kisa a shekarar 2014.

Tun dai shekarar 2010 shugaban dan shekaru 73 da haihuwa yake tsare a kurkuku, an kuma rataye shi da sanyin safiyar jiya Laraba, bayan kotun kolin kasar ta ki yarda da kokensa na hukuncin kisan tare da kin yarda ya nemi sassauci ga Shugaban kasar.

XS
SM
MD
LG