Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama yace tun ranar da ya kama mulki ya kuduri aniyar kashe Osama Bin Laden


Marigayi Osama bin Laden shugaban kungiyar al-Qaida
Marigayi Osama bin Laden shugaban kungiyar al-Qaida

Matakin farautar kashe shugaban kungiyar ta’addar Al-Qaida Osama Bin Laden shine a sahun gaba na abubuwan dana kuduri aniya yi tun lokacin da na zama Shugaban kasar Amurka.

Wannan ya fito ne daga bakin Shugaba Barack Obama, sai dai yace yadda za a gudanar da lamarin ne ya zama babban kalubalen da ake ta muhawara akai. Wannan shine karon farko da Obama ya yi cikakken jawabi akan kashe Bin Laden.

Tsawon watannin na bincike da bin diddigin jami’an leken asirin Amurka ne ya kai ga gano cewa Bin Laden din na boye a wani gidan bene mai hawa 3 dake da tsananin matakan tsaro a cikin birnin Abbotabad na kasar Pakistan.

Wani faifan bidiyon leken asiri ne ya nuna wani mutum mai siffar Bin Laden yana atisayen motsa jiki a harabar gidan. Shugaba Barack yace, sai dai matakin dauka ne mai wahala saboda gudun kuskure.

To amma yace a karshe tawagar tsaron Amurka suka nuna akwai yiwuwar ‘yan ta’adda ne a gidan bisa ga bayanan leken asirin, wanda kuma a karshe aka farwa gidan tare da nasarar hallaka wanda samfurin jininsa da aka gwada ya tabbatar da cewa Bin Laden aka kashe.

Hillary Clinton a lokacin tana Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka tace, a lokacin da suke kallon yadda ake kai harin kai tsaye daga fadar White House, ji take kamar zuciyarta zata fito waje saboda fargaba yadda zata kaya.

XS
SM
MD
LG