Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hunter Biden Ya Dakatar Da Harkokin Kasuwancinsa A Ukraine Da China


 Hunter Biden
Hunter Biden

Hunter Biden, dan tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Joe Biden, jiya Lahadi ya kare harkokin da ya yi a Ukraine da China, bayan da Shugaba Donald Trump ya yi kira ga kasashen biyu da su bincike harkokin kasuwancinsa, bukatar da ta sa Trump ke dabaibaye da binciken yiwuwar a tsige shi.

Dan na Biden, wanda mahaifinsa ke cikin wadanda ke kan gaba cikin 'yan takarar jam’iyyar Demokrat da ke neman kalubalantar Shugaba Trump a zaben Shugaban kasar a shekarar 2020, ya fada a cikin wata sanarwa da lauyansa ya fitar cewa duk da zargin da Trump ya yi cewa ya aikata rashin daidai yayin da ya ke daya daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na kamfanin samar da makamashi na Burisma a Ukraine na tsawon shekaru biyar, babu wata hukuma ta tsaro ta waje ko ta cikin gida da ta zarge shi da aikata rashin daidai.

Hunter Biden ya sauka daga mukamin mamban kwamitin gudanarwa na Burisma a watan Afrilun da ya gabata sannan, ba tare da yin wani bayani ba, ya ce zai bar kwamitin gudanarwa na kamfanin Harkokin Saka Jari na BHR (Shanghai) da ke China a karshen wannan wata na Oktoba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG