Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hushpuppi: Sufeto Janar Alkali Baba Ya Sa A Binciki Zargin Da Ake Yi wa Abba Kyari


Sifeton 'yan sandan Najeriya, Umman Alkali Baba (Facebook/Nigeria Police)
Sifeton 'yan sandan Najeriya, Umman Alkali Baba (Facebook/Nigeria Police)

“’Rundunar 'yan sandan Najeriya na kara jaddada cewa ta himmatu wajen tabbatar da adalci da karfafa dangantakar da ke tsakaninta da FBI da sauran abokanan hulda na kasa da kasa.”

Babban Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a Amurka take yi wa fitaccen dan sanda DCP Abba Kyari.

Hukumar ta FBI tana tuhumar Kyari da laifin hannu a ayyukan damfara da take binciken Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, matashin nan mai arziki dan Najeriya da hukumomin Amurkan suka kama suke kuma tuhumar yanzu haka a Amurka, bisa aikata laifukan da suka shafi zamba da damfara ta yanar gizo.

DCP Abba Kyari (Instagram/Abba Kyari)
DCP Abba Kyari (Instagram/Abba Kyari)

“Bayan da muka samu bayanai kan zargin tuhumar da hukumar hukunta manyan laifuka ta FBI take yi wa daya daga cikin jami’anmu, Sufeto Janar na ‘yan sanda IGP Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin a gudanar da binciken cikin gida kan lamarin.” Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta fitar dauke da sa hannun kakakinta CP Frank Mba ta ce.

“’Rundunar 'yan sandan Najeriya na kara jaddada cewa ta himmatu wajen tabbatar da adalci da karfafa dangantakar da ke tsakaninta da FBI da sauran abokanan hulda na kasa da kasa.” Mba ya ce.

Rundunar ‘yan sanda Najeriyar ta ce, za ta bayyanawa jama’a duk abin da ya taso dangane da wannan lamari idan ta kammala gudanar da bincikenta.

Hushpuppi ya shiga hannun Amurka ne a watan Yunin shekarar 2020 bayan da ‘yan sandan Hadaddiyar Daular Laraba suka kama shi a Dubai.

A wani zaman kotu da aka yi a ranar Laraba 28 ga watan Yuli a ci gaba da sauraren shari’arsa, Hushpuppi dan shekara 37, ya amsa aikata laifin halalta kudaden haram.

Yayin kuma bincike akan laifukansa ne ya bayyana cewa ya taba ba Kyari cin hanci a wata badakalar dala miliyan 1.1.

Amurka na tuhumar Hushpuppi kan ayyukan damfarar ta yanar gizo da ya yi ta miliyoyin daloli akan kamfanoni da daidaikun ‘yan kasuwa a Amurka da sassan duniya.

Ramon Abbas, Hushpuppi (Instagram/ Hushpuppi)
Ramon Abbas, Hushpuppi (Instagram/ Hushpuppi)

Kyari wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne, ya shahara a Najeriya da bisa yadda yake gudanar da ayyukansa da kuma nasarar da yake samu wajen kama gaggan masu aikata laifuka, lamarin da ya sa masa farin jini a kasar.

Sai dai ya musanta duk wani zargi da Hushpuppi ya yi, inda ya ce bai taba karbar kwabon Hushpuppin ba, illa taimaka masa da ya yi ya sayi kayan sawa da huluna na naira dubu 300.

“Ya ganni sanye da kayan kaftan da hula a shafukan sada zumunta sai ya ce sun ba shi sha’awa, sai na hada shi da mutumin da yake sayarwa, ya kuma tura wa mutumin kudin kai-tsaye.

“An kawo kayan da hula saiti biyar zuwa ofis dinmu ya kuma turo wani ya zo ya karba masa.” In ji Kyari.

A cewar Kyari, shekaru biyu da suka gabata, Hushpuppi ya taba kiran ofishinsu ya nemi a taimaka masa kan abin da ya kira barazana da wani yake yi wa iyalinsa a Najeriya.

“Ya turo mana lambar mutumin da yake yi wa iyalinsa barazana ya nemi da mu dauki mataki kafin ya yi wa iyalin nasa illa. Mun kuma bi diddigin mutmin muka kama shi, bayan binciken da muka yi sai muka gano cewa babu wani batun barazana ga rayuwar wani. Mun gano cewa ma abokanai ne suka samu sabani kan kudi. Sai muka sake shi.”

Ramon Abba, Hushpuppi (Instagram/ Hushpuppi)
Ramon Abba, Hushpuppi (Instagram/ Hushpuppi)

Kyari ya kara da cewa, “babu wani da ya nemi ko kwabo a hannun Abbas Huspuppi. Aikinmu ya karkakata ne kan ceto rayukan jama’ar da aka zargin ana yi wa rayuwarsu barazana.”

Hushpuppi mutum ne da ya dade yana jan hankulan ‘yan Najeriya kan yadda yake rayuwa ta alfarma wacce yake yawan wallafawa a shafinsa na Instagram mai mabiya miliyan 2.5.

Idan har kotun ta Amurka ta same shi da laifi, akwai yiwuwar a yanke masa hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekara 20.

XS
SM
MD
LG