Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hushpuppi Ya Zargi Abba Kyari Da Karbar Cin Hanci A Wata Badakalar Dala Miliyan 1.1


Abba Kyari, hagu da Abbas Hushpuppi, dama (Instagram/ Abba Kyari/Hushpuppi)
Abba Kyari, hagu da Abbas Hushpuppi, dama (Instagram/ Abba Kyari/Hushpuppi)

"Babu wani da ya nemi ko kwabo a hannun Abbas Huspuppi. Aikinmu ya karkakata ne kan ceto rayukan jama’ar da ake zargin ana yi wa rayuwarsu barazana.”

Binciken da wata kotun Amurka ta yi yayin shari’ar da ake yi wa dan Najeriyar nan Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, wanda ake tuhuma da aikata ayyukan damfara, ya tsumbula fitaccen dan sandan Najeriyar Abba Kyari cikin lamarin.

Wasu rahotanni sun ce tuni har kotun ta ba da umarni a kama Kyari, wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne a Najeriya.

Jami’an Amurka sun ce yayin da suke binciken Hushpuppi wanda biloniya ne mai rayuwa ta jin dadi, ya fada masu cewa ya taba ba Kyari cin hancin a wata badakalar sama da dala miliyan 1.1.

Sai dai a wani rubuta da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kyari ya musanta zargin na Hushpuppi, inda ya ce babu abin da ya hada shi da kan batun kudi illa taimaka masa da ya yi ya sayi wasu kayan sawa na na naira dubu 300.

“Ya ganni sanye da kayan kaftan da hula a shafukan sada zumunta sai ya ce sun ba shi sha’awa, sai na hada shi da mutumin da yake sayarwa, ya kuma tura wa mutumin kudin kai-tsaye.

“An kawo kayan da hula saiti biyar zuwa ofis dinmu ya kuma turo wani ya zo ya karba masa.” In ji Kyari.

Kyari ya kara da cewa, “ga wadanda suke murnar cewa an same mu da laifi suke ta yada labaran karya kan wasu makudan kudade, za su sake jin kunya domin babu wani abin da muke boyewa kan abubuwan da muka kwashe shekara 20 muna yi.”

A cewar Kyari, gabanin wannan cinikayyar kayan sawan, Hushpuppi ya taba kiran ofishinsu ya nemi a taimaka masa kan abin ya kira barazana da wani yake yi wa iyalinsa a Najeriya.

“Ya turo mana lambar mutumin da yake yi wa iyalinsa barazana ya nemi da mu dauki mataki kafin ya yi wa iyalin nasa illa. Mun kuma bi diddigin mutmin muka kama shi, bayan binciken da muka yi sai muka gano cewa babu wani batun barazana ga rayuwar wani. Mun gano cewa ma abokanai ne suka samu sabani kan kudi. Sai muka sake shi.”

Kyari ya kara da cewa, “babu wani da ya nemi ko kwabo a hannun Abbas Huspuppi. Aikinmu ya karkakata ne kan ceto rayukan jama’ar da aka zargin ana yi wa rayuwarsu barazana.”

A ranar Laraba 28 ga watan Yuli, Abbas ya bayyana a gaban kotu, ya kuma amsa cewa yana da laifi a zargin da ake masa na halalta kudaden hara.

A watan Yunin bara, ‘yan sandan Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa suka kama Hushpuppi suka mika shi ga jami’an binciken manyan laifuka na FBI na Amurka, bisa zargin yin almundahanar euro miliyan 350 ta yanar gizo.

Idan har aka same shi da laifi, akwai yiwuwar a yankewa Abbas Hushpuppi hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekara 20.

Abbas Ramon dan shekara 37, ya yi fice ne a Najeriya a shafin Instagram inda yake da mabiya sama da miliyan 2.5, saboda irin rayuwa ta alfarma da jin dadi da yake yi.

XS
SM
MD
LG