Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ibrahimovic Ya Shiga Sahun 'Yan Wasan Da Suka Zura Kwallaye 300


Zlatan Ibrahimovic

Ibrahimovic, wanda dan asalin kasar Sweden ne, ya shiga wannan rukunin ne bayan da ya zura kwallonsa a karawar da suka yi da Udinese a gasar Serie A ta Italiya.

Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic ya zama dan wasan kwallon kafa na uku da ya zura kwallaye 300 a manyan gasa guda biyar da ake bugawa a nahiyar turai.

Hakan na nufin ya bi sahun dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo da dan wasan PSG Lionel Messi wadanda tuni suka shiga wannan rukuni.

Ibrahimovic, wanda dan asalin kasar Sweden ne, ya shiga wannan rukunin ne bayan da ya zura kwallonsa ta 300 a kusan lokacin kammala wasan da suka kara da Udinese a gasar Serie A ta kasar Italiya

Yanzu yana da kwallo 73 a kungiyar ta Milan da 57 a Inter, 23 a Juventus duk a gasar ta Seria A.

Sannan yana da kwallo 113 a PSG da ke gasar Ligue 1 ta Faransa, 18 a Manchester United da ke gasar Premier League ta Ingila 16 a Barcelona da ke gasar La Liga a Sifaniya kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG