Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan An Inganta Sha'anin Noma A Duba Batun Tsaro Kuma-Manoma


Manoma a gona
Manoma a gona

Manyan manoma da ‘yan kasuwa a Najeriya sun fara mayar da martani game da kokarin inganta cinikin kayan abincin da aka noma a cikin gida, da ya sa shugaba Buhari ya ba shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emefiele umurni da ya daina bawa masu shigowa da kayan abinci daga kasashen waje tallafi.

Wannan ba shine karo na farko da mahukuntan kasar a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari za su dauki irin wanan mataki na hana a shigo da kayan abinci daga kasashen waje ba, domin daga hawansa mulki a shekara 2015 aka haramta shigowa da wasu kayayyaki 41 wadanda ake ganin ana samun su a cikin gida Najeriya.

Shugabar Mata Manoma a Jihohin Arewa Bilkisu Mohammed ta ce wanan umurni yana da kyau sai dai ya bar baya babu zani, domin masu kama mutane su yi garkuwa da su sun hana mata yin noma, ta yi kira ga shugaba Buhari da ya tashi tsaye ya yi maza maza ya magance harkar tsaro domin a ci moriyar wanan umurni, in ba haka ba zai yi wuya a ci nasara.

Shi ma mataimakin shugaban kungiyar masu masana'antu da aikin gona ta kasa Sanusi Maijama’a Ajiya ya ce umurnin yana da kyau sai dai ba lallai ne mutane su bi ba sai an dauki mataki, saboda so tarin yawa manoma ba su samun tallafin da ake bada wa domin su.

Kwararre a fanin tattalinarziki Yusha’u Aliyu ya ce duk kasar da ta keso ta ciyar da kanta kuma a samu zaman lafiya dole ne ta dauki irin wannan mataki domin ta samu kudaden shiga daga kasashen waje saboda farfado da tattalin arzikin ta.

Wakiliyarmu a Abuja Medina Dauda ta hada mana rahoto akan batun.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG