Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Ban Nemi Tsayawa Takara Ba, Na Ci Amanar 'Yan Najeriya - Osinbajo


Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo (Twitter/ Laolu Akande)
Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo (Twitter/ Laolu Akande)

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa ganin yadda ya samu isasshen ilimi da kwarewa a sha’anin mulki, sannin jiga-jigai masu fada a ji a ciki da wajen Najeriya, idan bai tsaya neman takarar mulkin kasar a shekarar 2023 ba zai zama tamkar ma ci amana ga Najeriyar ne kawai.

Mataimakin shugaba Buharin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi yayin wata ziyarar da shi da tawagarsa su ka kai wa gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, da wasu masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC a jihar kamar, yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.

Haka kuma, Osinbajo ya ce baya ga mukamin da yake rike da shi na Mataimakin Shugaban kasa, kasancewar ya rike mukamin mukaddashin shugaban kasa na tsawon watanni ya kuma ba shi kwarewar da ake bukata wajen jagorantar Najeriya.

Osinbajo ya ce kusan kullum mutane da dama na sadaukar da rayuwarsu domin ci gaban kasar, kuma idan bai yi amfani da duk abunda ya koya a tsawon lokacin da ya ke rike da mukamin Mataimakin Shugaban Kasa ba har ya yi ritaya zuwa Legas ko mahaifarsa wato Ikenne don in ya rubuta tarihinsa kawai, zai kasance ya yi wa kasar babban rashin adalci ne.

A cewarsa, a halin da ake ciki a yanzu dama ta zo, idan aka yi la’akari da gogewar da yake da ita, alaka, da huldar da yake da ita a cikin gida da waje, nauyi ne ya rataya a kansa na ya ci gaba da aiki a inda maigidansa, Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya.

Duk da cewa Osinbajo na da yakinin cewa babu mutumin da zai iya zama wani abu sai da yardar Allah, shi ya sa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa neman takarar Shugabancin Kasar bisa ga cewa ya yi fiye da watanni bakwai a matsayin Shugaban Kasa na riko wato Mukaddashin Shugaba Buhari kenan.

Lamarin da ke zama wani babban nauyi a matsayin mukaddashin shugaban kasa, in ji Osinbajo.

A bangaren mai masaukin bakin, gwamna Akeredolu ya ce wakilan jihar na kaunar Osinbajo da girmama shi saidai Allah ne kawai ke ba wa wanda ya so mulki.

Idan Ana iya tunawa, tun bayan da farfesa Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa neman takarar shugabancin kasar a ranar 11 ga watan Afrilu ya ke ta zagayen ziyara a fadin kasar domin neman goyon bayan al’umma na cimma burinsa na gadar kujerar maigidansa shugaba Muhammadu Buhari.

Wasu masana siyasa dai na ganin lokacin da Osinbajo ya bayyana aniyarsa din bai dace ba duba da yadda wasu ‘yan kasar ke tsare a hannun yan bindiga musamman ma matafiyan cikin jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna da 'yan bindigar suka tarwatsa wani bangaren shi, kuma daga bisani suka yi awon gaba da matafiya da dama baya ga wadanda suka bindige har lahira.

XS
SM
MD
LG