Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ijabula Seltimari Ya Tsallake Rijiya da Baya a Garin Izghe


Barnar da Boko Haram tayi wa garin Izghe, Fabrairu 15, 2014.

Idan ba'a manta ba garin Izghe a jihar Borno ya sha samun hari daga 'yan Boko Haram lamarin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dama da ma dukiyoyi. To amma a cikin ikon Allah wani Ijabula Seltimari ya rayu bayan ya sha harbi.

Wakilin Muryar Amurka ya zanta da wani Ijabula Seltimari dan asalin garin Izghe wanda aka kashe 'yanuwansa kafin a harbeshi amma kuma Allah cikin ikonsa ya bar shi ya rayu. Yanzu yana sansanin 'yan gudun hijira a Bole dake cikin jihar Adamawa.

Ijabula Seltimari yace lokacin da 'yan Boko Haram suka kawo hari a garin Izghe da misalin karfe tara na dare shi yana kwance a daki sai suka buga kafar dakinsa da gaya masa cewa idan bai bude ba zasu fasa kofar da bindiga domin sun zo ne su kasheshi.

Yana bude kofar dakinsa sai suka tambayeshi takardar motarsa da na babur da ya saya. Duk ya kwasa ya basu. Kana suka sake tambayar abun da yake dashi sabili da haka duk kudaden dake hannusa nashi da na wasu ya basu. Amma sai da suka sakawa motarsa wuta.

Bayan sun kwace kudadan dake hannunsa sai suka sa ya kwanta kasa. Mutane da suka fito, yayansa da kakansa da matar yayansa rike da jinjiri da makwaftansa duk suka harbe har lahira.

Duk da harbin da suka yiwa Ijabula sau biyu Allah ya rayar dashi amma gefen jikinsa daga hannun dama ya mutu. Yace baya jin komi. Ya godewa Allah da ya bashi rai sai dai yanzu abun da zasu ci shi ne matsala.

Ga rahoton Ibrahim Alfa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG