Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ilhan Omar Ta Roki Gafara Game Da Kalaman Kin Isra'ila


Ilhan Omar 'yar majalisar dokokin Amurka
Ilhan Omar 'yar majalisar dokokin Amurka

Wata sabuwar ‘yar majalisar dokokin Amurka ‘yar asalin Somalia da ta yi gudun hijira zuwa nan Amurka, ta nemi afuwa a jiya Litinin a kan kalamanta na sukar lamirin Yahudawa, lamarin da yasa ‘yan jami’iyyun Republican da Democrats suka yi tir da kalaman.

‘Yar majalisar na bangarn Democrats, Ilhan Omar wacce take wakiltan wata gunduma a jihar Minnesota dake tsakiya maso yammacin Amurka tsawon makwanni biyar, tace wani rukunin ‘yan Isra’ila mai kamun kafa a nan Amurka, wato kungiyar huldan Amurka da Isra’ila tana sayen ‘yan majalisar domin bada goyon bayansu ga kasar Isra’ila.

Ta yi wadannan kalaman ne a wani sakon Twitter a ranar Asabar, tana mai cewa goyon baya da ‘yan majalisar ke baiwa Isra’ila suna yi ne saboda kudin dake fitowa kungiyar AIPAC mai kare akidojin Yahudawa, koda yake kungiyar bata taiamakawa yakin neman zaben ‘yan siayasar Amurka kai tsaye, amma kuma mambobinta zasu iya taimakawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG