Ta wani gefen kuma, a jawabinsa na "halin da kasa ke ciki" da ya gabatar jiya a gaban ‘yan-Majalisun Dokokin Amurka, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana game da yake-yaken da sojojin Amurka suka sami kawunansu a ciki na tsawon shekaru da dama.
Trump ya yi la'akari da makudan kudaden da Amurka ke kashewa a yaƙe-yaƙen Afghanistan da Iraq, wanda ya haifar da mutuwar sojoji kusan 7,000 na Amurka tun shekara ta 2001.
Ya ce bayan shekaru da yawa na yaki a Afghanistan, yanzu shine lokacin neman zaman lafiya. Kuma ya ce kungiyar Taliban ma na son haka. Haka kuma shugaban ya tunatar da cewa ya bada umurnin janye sojojin Amurka daga Syria, inda tun shekarar 2014 suke yaki da dakarun kungiyar ISIS.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum