Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Illar Cutar Daji Idan Ba a Dauki Matakin Gaggawa Ba


Matar gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Zainab Bagudu, ta baiyana cewa gidauniyar da ta ke jagoranta mai suna “MEDICAID” za ta gudanar da sabon gangami a bana ta hanyar tattaki a tsakiyar Abuja don fadakar da jama’a illar cutar daji da kan hallaka majinyaci in ba a samu matakin wuri ba.

Zainab Bagudu wacce ke zantawa da manema labarai a Abuja, ta ce ranar Asabar din karshen watan nan za a gudanar da tattakin da gaiyatar mutane musamman ma’aikata da ba sa motsa jiki su fito don takawa da ‘kafa tsawon kilomita 10.

Gidauniyar dai da kan tallafawa masu fama da cutar daji musamman mata da kan samu matsalar a maman su da mahaifa, na samun labarun masu jinyar a birane da karkara, inda ta kan tura a kai mu su dauki.

Zainab Bagudu ta ce maganin ya na da tsadar gaske, don haka ya dace mata su rika duba maman su duk wata don fahimtar lafiya kalau su ke ko da wata alamar larura.

Ita ma hukumar lafiya matakin farko ta taraiya ta bukaci mutane su rika lura da alamun cuta da wuri kamar shan inna da a ke neman gamawa da ita.

Dakta Saidu Adamu, shine jami’in daukin gaggawa na yaki da shan inna, ya ce da zarar an samu labari a kan tura jami’ai don tabbatarwa da daukar matakin da ya dace.

A Najeriya ba mamaki ka ga ginin asibiti amma ba lalle ne akwai wadatattun likitoci da magunguna ba da hakan kan sanya masu hannu da shuni tafiya asibitocin kudi, wasu talakawa kuwa su rika tunkarar magungunan gargajiya don saukin samu.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG