Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Alfahari Da Karfin Da Amurka Ta Kara A Lokacina


Shugaba Obama
Shugaba Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya fadi jiya cewa kasar, a ta bakinsa, "ta gyaru kuma ta fi karfi" fiye da lokacin da ya zama Shugaba a 2008, ya na mai nuni da magance matsalar tattalin arzikin da ya gada, da kuma bullo da hanyar inganta fannin lafiya da ya yi da kuma halatta auren 'yan luwadi a matsayin nasarorin da Amurkawa su ka samu bisa bishewarsa.

Wannan bangare na jawabinsa ya janyo sowa ta yabo daga dubban mutanen da su ka taru a birnin Chicago, a inda bai da nisa daga wurin da ya yi jawabinsa na amincewa da zama Shuagaban kasa a daren ya ci wa'adin farko na Shugabancin kasar.

Ana kasa da sati biyu a rantsar da Shugaba mai jiran gado Donald Trump, Obama ya umurci hadimansa da su tsara jawabi irin wanda zai yi tasiri kan dukkan Amurkawa, ciki har da wadanda su ka zabi Trump.

Obama ya fadi a jawabinsa cewa ya rage ga Amurkawa su tabbatar da cewa gwamnati ta magance kalubalen da ke fuskantar kasar kuma ya ce shi kam ya himmantu ga ganin cewa an mika mulki ga gwamnati ta biye cikin nasara.

Obama ne bakar fatan farko da ya zama Shugaban Amurka, ya kuma yi nuni da yadda bayan zabensa mutane da dama sun yi fatan cewa an yi bankwana da wariyar launin fata a Amurka. To amma kash sai gashi har yanzu batun bambancin launin fata na cigaba da raba mutane, sannan ya jaddada bukatar a karfafa dokar hana nuna wariya.

XS
SM
MD
LG