Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Cikin Koshin Lafiya Duk Da Cewa Na Killace Kai Na - Merkel


Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce tana cikin koshin lafiya a inda ta ke kebe a gidanta, tun bayan da ta hadu da wani likita, wanda ya kamu da cutar Covid-19, a cewar mai magana da yawunta.

Steffen Seibert, mai magana da yawun shugabar, ya fada wa manema labarai cewa Merkel tana ci gaba da gudanar da ayyukanta daga gida.

Ya kuma ce tana kuma magana da dukkan ministocinta domin ci gaba da gudanar da muhimman ayyukan kasar.

Ita dai Merkel ta killace kanta da kanta ne a karshen makon da ya gabata, bayan da ta sami labarin cewa likitan da ya yi mata allurar rigakafi, an tabbatar da cewa ya kamu da cutar Covid-19.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG