Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina da ciki menene ya kamata in yi- ko kuma kada in yi- domin kula da kaina da jaririn dake ciki na? (chigabawa)


Wadansu mata masu ciki suna zaune a asibiti

Ki kiyaye wadannan umarni domin kula da lafiyarki da ta jaririn dake girma a cikinki

Ki kiyaye wadannan umarni domin kula da lafiyarki da ta jaririn dake girma a cikinki:

Abubuwan da zaki yi ko kuma kiyaye na lafiya

  • ·Ki rika zuwa awo a kai a kai. Ko wannan ce haihuwarki ta farko ko ta uku, kula da lafiyarki yana da muhimmanci ainun. Likita zai gwada ya tabbata ke da jaririn kuna cikin koshin lafiya a kowanne lokaci kika je ganin likita. Idan akwai wata matsala, daukar mataki a kan lokaci zai taimake ki da jaririnki.
  • ·Ki sha kwayoyin magani mai gina jiki ko magungunan da ake bayarwa a lokacin awo tare da mikogram 400 zuwa 800 (400 to 800 mcg or 0.4 to 0.8 mg) na folic acid kowacce rana. Folic acid yafi muhimmanci a farkon daukar ciki amma ki ci gaba da sha har lokacin haihuwa.
  • ·Ki tambayi likita kafin daina shan magani ko kuma fara shan wani sabon magani . Wadansu magunguna suna da hadari a lokacin da mace take da ciki. Ki sani cewa, wadansu magungunan da ake saya a kemis, ko kuma na gargajiya suna da illa. Sai dai kuma rashin amfani da magunan da kike bukata shima yana iya zama da illa.
  • ·Kada ki dauki hoton wani bangaren jiki a asibiti (x-rays). Idan ya zama dole a yi maki wani aiki a hakori ko kuma gwaji ki shaidawa likitan kina da ciki sabili da a kula da kyau.
  • ·Idan akwai maganin rigakafin mura, kiyi domin mata masu ciki sukan yi fama da mura da wadansu lokuta sai an kwantar da su a asibiti.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG