Accessibility links

Ina da ciki menene ya kamata in yi ko kuma kada in yi domin kula da kaina da jaririn dake ciki na? (karshen bayanai)


Wasu mata masu ciki suna zaune

Abinda ya kamata ki yi ko kuma ki kiyaye da ya shafi muhalli

  • ·Ki nisanci magungunan kwari kamar maganin sauro da fenti. Ba dukan magunguna suke da gargadi da ya shafi masu ciki ba. Idan baki da tabbacin ko maganin bashi da illa, ki tambayi likita kafin kiyi amfani da shi. Ki yi Magana da likita idan kina tunanin maganin da aka yi amfani da shi a wajen aikinku yana da illa.
  • ·Idan kuna da mage, ki tambayi likita dangane da cutar da ake dauka daga mage. Wani lokaci ana samun wannan cutar ne daga kashin mage. Idan ba a sami magani ba cutar tana iya sa a haifi jariri da nakasa. Zaki iya rage hatsarin kamuwa da cutar ta wajen yin nisa da kashin mage da kuma sa safar hannu lokacin da kike aiki a lambu.
  • ·Kada ki taba bera da kashin bera ko fitsarinshi, ko inda yake kashi. Bera yana daukar cutar da zata kasance da illa ko kuma kashe jaririnki dake ciki.
  • ·Ki dauki matakan da zasu hana ki rashin lafiya, kamar wanke hannu a kai-a kai.
  • ·Kada ki tsaya kusa da mai shan taba.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG