Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Ina Tasirin Siyasar Karba-karba?


APTOPIX Nigeria Election
APTOPIX Nigeria Election

To da yake matasa sun samu baki sosai a babban zabe dake gudana a Najeriya, Ahmed Adamu shine shugaban kungiyar matasan kasashen da Britaniya ta raina.

“Saboda gaskiya ban-bance ban-bance na al-umma da muke da shi, kuma kowa yana so ya bada irin nashi gudunmuwar, ina tunanin kamar hakan ya dace, saboda shine zai kawo masalaha, wani ba zai tunanin kamar an barshi a baya ba” a cewar Ahmed Adamu.

To amma kasashe da suka cigaba kamar Amurka, me yasa basu da siyasar bangaranci da banbance banbance duk da cewa kasar ta kunshi mutane iri-iri.

Dr. MK Hassan, masanin harkokin siyasa ne da kimiya daga Jami’ar Penn State “idan mutane suka ga, ana yi musu adalci, ko da dan wani kabila ne, idan wannan babu shi, sai ka ga siyasa ya koma na bangaranci da addini. Amma idan aka sami adalin shugabanni, wanda kawai koma kai dan ina ne, ko wani dan addini ne, ko kabila idan yana yin adalci, sai kaga wannan duka wannan abu ya mutu”.

Masu magana suka ce “abunda babba ya hango, yaro ko ya hau rimi ba zai gane shi ba”. Dan Masanin Kano, Dr. Maitama Sule yayi tsokaci.

“Na taba fadi nake cewa da za’a dauki akidar Sardauna, da duka abunda ya dame mu a Najeriya zamu samu amsa. Rikici ne na addini, rikice ne na kabila, rikici ne na siyasa, na zamantakewa ne, duk akidar Sardauna zata yi maganinsa”, a cewar Maitama Sule.

Sai dai a halin yanzu shuwagabanni sun fara dawowa da rakiyar amfani da ban-banci a siyasance. Ga gwamnan Jihar Kano mai barin gado Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

“Zaka ji ana maganan Kirista. Zaka ji ana maganar Musulmi, zaka ji ana maganar Kudu, ana maganar Arewa. Ana maganar kabilu da sauransu. Duka wadannan, a lokacin Demokradiyya bai kamata a yi maganar su ba. Du wannan, abu ne wanda yake na rauni, wanda shugabanni in suka samu rauni, sai suyi ta shigo da irin wannan abubuwa, kuma shigo da su shi ke kawo fititunu da rigingimu. Mutane suyi ta rasa rayukansu, a yi ta ji wa mutane ciwo, mutane suyi ta asarar dukiyarsu, maimakon a yi gaba, sai kaga ana ta zagayawa har ma a koma baya”.

To tambayar anan itace yaushe za’a cire banbance banbance a harkokin siyasa a nahiyar Afirka?

Yanzu da siyasar Najeriyan ke sauyawa, sai mu zuba idanu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG