Burin da India ta sa a gaba na ganin ta tura jirgin da baya dauke da matuki zuwa Duniyar wata domin gudanar da bincike, ya samu cikas, bayan da hukumar kula da bincike a sararin samaniyan kasar ya gaza tuntubar jirgin na ta mintina kadan gabanin ya sauka a duniyar watan.
Wannan dai babban koma-baya ne ga kasar ta India, wacce ta so ta bi sahun kasashe uku kacal da suka yi nasarar tura jiragensu zuwa duniyar watan – wato Amurka da Tsohuwar Tarayyar Soviet da kuma China.
Miliyoyin jama’ar kasar ne suka raba dare a gaban akwatunan talbijin dinsu domin kallon yadda jirgin zai sauka a yau Asabar kamar yadda aka tsara.
Wannan yunkuri shi ne na biyu kuma mafi sarkakiya da kasar ta fuskanta na tura jirginta da zuwar Duniyar watan, wanda aka wa lakabi da “Chandarayaan – 2.”
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 29, 2023
Ukraine Ta Kaiwa Rasha Wani Mummunan Hari
-
Maris 29, 2023
Kasar Azerbaijan Ta kaddamar Da Binciken Harin 'Yan Ta'adda