Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

India Ta Killace Wani Mutum Da Ake Zargi Ya Kamu Da Kyandar Biri


Gargadin cutar Kyandar Biri a filin jirgin sama na Tangerang
Gargadin cutar Kyandar Biri a filin jirgin sama na Tangerang

India ta ba da rahoton killace wani mutum da ake zargin ya kamu da cutar kyandar biri, inda ta tabbatar da cewa kasar da tafi yawan al’umma a duniya tana da kwararan matakai da ta dauka, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Babu wanda aka tabbatar ya kamu da cutar kyandar biri a India, kasar mai yawan mutum biliyan 1.4.

Ma’aikatar lafiyar ta fada a cikin sanarwa cewa “wani matashi mara lafiya, wanda ya yi balaguro daga kasar da yanzu haka ke fama da yaduwar cutar kyandar biri ne, a ka bayyana a matsayin wanda ake zargi da kyandar biri.”

Sanarwar ta kara da cewa “an killace mara lafiyan a wani asibiti kuma a halin yanzu yana murmurewa,” ta kara da cewa an dauki samfurinsa “ana gwadawa don tabbatar da ko yana dauke da kyandar biri.”

Sai dai ba ta ba da wasu bayanai ba na inda mai yiwuwa ya kamu da cutar.

Sanarwa ta kara da cewa, “babu wani abin damuwa da zai ta da hanakli.”

“Kasar ta shirya tsaf don tunkarar irin wannan killacewa balaguro da ke da alaka da cuta kuma tana da kwararan matakai don kula da kawar da duk wata barazanar hadari.”

Sake bullar cutar kyandar biri da gano wani sabon nau’in cutar mai saurin yaduywa a Jamhuriyar Dimokoradiyyar Congo, wanda aka yi wa lakabi da Clade 1b, ya sa hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana matakin fadakarwa mafi girma a duniya a ranar 14 ga watan Agusta.

Haka kuma an samu bullar cutar a nahiyoyin Asiya da Turai.

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG