A Indiya, gobe Juma’a ake shirin aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wasu maza su hudu da suka aikata laifin fyade da kuma kisan wata mata a cikin wata motar bas ta birnin New Delhi a shekarar 2012, duk da cewa lauyoyi sun yi yinkurin jinkirta yanke hukuncin.
Lamarin fyaden ya haddasa zanga-zanga a Indiya da ma kasashen waje, abinda kuma ya janyo kiraye-kiraye daga masu fafutika da suka kai ga yin dokar hukunci mai tsanani akan masu aikata laifin fyade da kuma kafa kotuna na musamman da zasu kula da laifuffukan da suka shafi cin zarafin mata.
Shekaru uku da suka gabata Kotun Kolin Indiya ta amince da hukuncin kisan da aka yanke wa mazan su hudu kuma ta yi watsi da bukatar sake nazarin hukuncin cikin shekaru biyu da suka gabata.
Tun da farko, mutum 6 aka tuhuma da aikata laifin, ciki har da wani matashi dan shekara 18. Amma an ce wai mutum na shida a cikinsu ya hallaka kansa a gidan yari, jim kadan bayan da aka fara shari’ar. An yanke wa matashin hukuncin dauri tsawon shekara 3 a wata cibiya yayin da sauran kuma za a rataye su gobe Juma'a da safe.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 18, 2021
Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Na Bukatar Sabon Salon Gudanarwa-Dr. Ngozi
-
Fabrairu 18, 2021
Guterres Ya Yi Kiran a Samar Da Tsarin Bai Daya Na Rigakafin Coronavirus