Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indiya Tayi Gwajin Makami Mai Linzami Mai Dogon Zango


India ta sami nasarar gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango da ake kira Agni-V, wanda zai iya afkawa cibiyoyi masu nisan kilomita dubu biyar,wanda zai iya kaiwa ga yankin arewacin China.
Jiya Litinin India tayi gwajin makamin mai tsawon mita 17.5 da nauyin ton 50 wanda ake harbawa daga doron kasa,an gudanar da gwajin ne daga wani tsibiri da ake kira Abdul kalam, ba nesa daga gabar ruwan jahar da ake kira Odisha, makamin ya culla can wajajen ruwayen kasar Australia.
Kirar farko na wannan makami mai linzami da aka habaka cikin shekaru 10 da suka wuce, za'a iya farmaki da su ko ina cikin kasar Pakistan, mabkwaciyarta kuma abokiyar hamayyarta a kudancin na Asiya. Kasashen biyu sun gwabza yaki har sau uku, kuma ahalin yanzu zaman dar dar tsakanin kasashen biyu yayi tsanani. Ita ma Pakistan tana da makamai masu linzami.
Wani mai fashin baki kan harkokin tsaro yace makami mai linzamin dake cin dogon zango, India ta kera shi da tunanin China a zuciyarta, domin tana kallon kasar a zaman mai mata barazana.

XS
SM
MD
LG