Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: INEC Ta Tabbatar Da Gudanar Da Zabe a Karamar Hukumar Quanpan


A yau Talata ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar plato, ya tabbatar da cewa za'a gudunar da zaben 2019 a garin Quanpa, bayan offishin hukumar ya kama da wuta ya yin da wasu katunan mutane da kayan aiki suka kone.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Filato, ta ba da tabbacin gudanar da zabe a karamar hukumar Quanpan, inda gobara ta lashe wassu kayayyakin zabe ciki har da katunan zabe kusan dubu shida.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Filato, Malam Hussaini Halilu Pai, ya ce tuni suka dauki sunayen wadanda gobarar ta shafi katunan su, ta kuma samar da sauran kayayyakin da suka kone don tabbatar da cewa kowa ya sami damar yin zabe.

Mataimakin sakataren majalisar mashawarta kan harkokin jam'iyyu, Sabastine Pyoklam, ya shawarci masu kada kuri'a da su kai rahoton duk wani abin da suka gani ba dai-dai ba, maimakon daukar doka a hannunsu.

Salisu Idris mai kilishi Bokkos, ya baiwa jama'a shawara da su bi chanchanta wajen zaben shuwagabanni.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG