Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Dage Zaben Najeriya


INEC
INEC

Hukumar Zaben Najeirya INEC, ta dage zaben shugaban kasar da za a yi a yau Asabar zuwa 23 ga watan Fabrairu.

A wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar dazun nan da misalin karfe 2 na dare agogon Najeriya, Shugaban hukumar Prof. Yakubu Mahmood, ya ce bayan lura da wasu batutuwa da suka shafi shirye-shiryen zaben, hukumar ta lura da cewa, gudanar da zaben ba zai yiwu ba.

“Wannan mataki da hukumar ta dauka bai zo mata da dadi ba, amma ya zama dole a dauke shi, domin zai taimaka wajen samar da sahihin zabe.” Inji Prof. Mahmood.

Ya kara da cewa, “hukumar za ta zauna da masu ruwa da tsaki domin ta fada masu halin da ake ciki a yau da misalin karfe 2 na rana (agogon Najeriya).”

A da, an tsara za a yi zaben na Najeriya a yau Asabar bayan da aka kammala yakin neman zabe a ranar Alhamis.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:18 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG