Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC, Ta Yarda Jam'iyyar APC Ta Yi Zabe A Zamfara


INEC

Bayan kotuna sun yanke hukunci, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, da ake kira INEC, ta Amince da Jam’iyyar APC ta gudanar da zabe a Jihar Zamfara.

A jiya ne Kotun Daukaka Kara ta Nigeria, ta yanke hukuncin cewa reshen APC na jihar Zamfara zai iya tsayarda 'yan takarar sa na gwamna da na 'yan majalisun dokokin tarayya a zaben da za ayi gobe Assabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Wannan na zuwa ne bayan cece-kuccen da ya barke a tsakanin bangarorin 'yan takarar jam'iyyar ta APC, inda aka samu baraka tsakanin gwamnan jihar Abdul'aziz Yari da wani gungun 'yan takara su takwas da suka hada da Dan majalisar dattawa Kabir Marafa, da Dauda Lawal, da sauransu.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG