Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC Tace Ba'a Kammala Zaben Gwamna A Kogi Ba


(File Photo)

Hajiya Amina Zakari, Kwamishinar Hukumar ta tabbatar da haka a zantawa da manema labarai.

Baya ga rashin kammala zaben saboda ba'a yi zabe a wasu wurare ba, da kuma yawan kuri'a da suka lalace, kwatsam sai ga labarin cewa dan takarar Gwamna a tutar jam'iyyar APC Yerima Abubakar Audu Allah, Ya yi masa rasuwa. Lamari da ya jefa zaben baki daya cikin rudani.

Hajiya Amina Zakari, wacce tasa ido kan zaben, tace akwai ma wurare da aka hana ma'aikatansu zuwa. Saboda haka tilas ne a gudanar zaben nan da mako biyu.

Tunda farko wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari, ya ziyarci gidan marigayi Abubakar Audu, inda mutane suke bayyana alhininsu kan wannan rashi da aka yi.

Wasu suna kuka da da hawaye.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG