Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Tasha Alwashin Gudanar Da Sahihin Zabe a Jihar Ekiti


Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria).
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria).

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar (INEC) tace ta shirya tsaf don ganin ta gudanar da sahihin zaɓen gwamna a jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Najeriya.

Yayin jawabinsa a taron masu ruwa da tsaki kan zabe a Ado-Ekiti babban birnin jihar, shugaban na INEC Farfesa Mahmood Yakubu yace hukumar zata tabbatar kuri'ar mutane ce zata baiwa duk wanda yaci nasara, ba aringizo ko magudin zaɓe ba.

Jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Najeriya, na cikin jihohi shida da ake gudanar da zaɓe ba lokacin babban zaɓe ba.

A ranar Asabar mai zuwa ce dai masu zabe zasu je runfunan zaɓe a jihar don zaɓan gwamnan da zai jagoranci jihar na shekaru huɗu.

Cikin shirye-shiryen ganin an gudanar da zaɓen lami lafiya hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta haɗa taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe a Ado-Ekiti babban birnin jihar, don tattaunawa tare da baiwa juna shawara don ganin anyi zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Yayin hira da Muryar Amurka Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu yace hukumar sa a shirye take don ganin anyi sahihin zaɓe.

A nasa ɓangaren, babban sufeta janar na ƴan sandan Najeriya Alkali Usman Baba yace, akalla ƴan sanda 17,000 ne zasuyi aikin tabbatar da anyi zaɓen ba tare da wani tashin hankali ba.

Yan takara dama shugabannin jam'iyyu daban-daban sun nuna amincewarsu da shirye-shiryen hukumar zaben mai zaman kanta, duk da cewa wasu mazauna jihar na cikin zulumi saboda matsalar tsaro dake addabar jihohi masu makwabtaka da Ekiti.

XS
SM
MD
LG