Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kayan Lambun da Taraba Ke Samarwa Sun Kai Na Kasashen Ketare Inganci


Shingen Lambu (Green House)
Shingen Lambu (Green House)

Gwamnatin Jihar ta kafa wuraren shukar zamani don samar da karin kudaden shiga ganin cewa abinda take samu daga tarayya ba ya wadatar da ita.

Gwamnatin jihar Taraba ta soma safarar kayan lambu zuwa manyan kantunan sayar da kayan gwari a manyan biranen Najeriya wadanda take nomawa rani da damina a shingayen lambunan zamanin na GREEN HOUSE arba’in, da ta kashe sama da Naira biliyan biyu da zai samarwa jihar kudaden shiga don rage dogaro da kason dake fitowa daga gwamnatin tarayya da jihohi ke amsa kowace wata.

Sakamakon inganci da karbuwa da kayan da ake nomawa a lambunan ke samu kasuwannin da ke jihohin Legas, Cross River da birnin tarayya Abuja, gwamnatin jihar na duba hanyoyi masu inganci na dakon kayan lambun ta jiragen sama inji gwamnan jihar Taraba Arch. Darius Dickson Ishaku.

Akwai matasa sama da dari biyu dake amfana daga ayukan yi da koyon sabbin dabarun noma a lambuna zamanin da gwamnati jihar Taraba ta kafa tare da taimakon shawarwarin kwararru kan harkar noman lambu ‘yan kasar Isra’ila.

Lambunan zamani da gwamnati ta kafa na anfani da na’ura masu kwakwalwa, injunan ban ruwa, feshin magani da takin zamani da kayan aiki masu amfani da hasken rana wajen samar da wutan lantarki kamar yadda shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Taraba Mal. Abdulrahaman Adamu, ya bayana.

Kwamishinan ma’aikatar noma ta jihar Taraba Dokta Ishaya Kasa ya shaidawa wakilin muryar Amurka Sanusi Adamu, cewa bayanai da suke samu daga kasuwannin da suka kai hajarsu sun nuna ingancinsu na daidai da wadanda ake shigowa da su daga ketare. Ya ce kudaden da jihar ke samu daga kason gwamnatin tarayya baya wadatarwa shi yasa gwamnati ta tsayarda shawarar neman hanyoyin bunkasa tattalin arziki’.

Mal. Abdullahi Kanti mazaunin karamar hukumar Karin Lamido ya bayyana shingayen lambuna da gwamnatin jihar Taraba ta kafa sun rage zaman kashe wando musamman tsakanin matasan jihar wadanda ya ce zasu habaka sana’ar noma da samar da kudaden shiga a hanun jama’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG