Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Inganta Shirin Tsugunar Da Tubabbun 'Yan Boko Haram


Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

An lura cewa akwai bukatar inganta shirin nan na sake tsugunar da tubabbun 'yan Boko Haram. Kungiyoyin raji na ganin kyautata masu zai dada kwadaita ma masu niyyar tuba.

Shekaru shida da suka gabata, hare-haren kunar bakin waken da kungiyar Boko Haram ke kai wa a arewa maso gabashin Najeriya da sauran kasashe makwabta, sun kai wani matakin na la-haula, inda suka rika amfani da mutanen da suka hurewa kunne, wajen kai hare-hare a kasuwanni da makarantu da sauran wuraren taron jama’a.

A wani mataki na shawo kan wannan matsala, hukumomin Najeriya, sun dukufa wajen ganin sun karfafa gwiwar mayakan kungiyar su rika mika wuya, domin a sauya musu tunani.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama, sun fara dasa alamar tambaya, kan tasirin wannan shiri, wanda suka ce yakan kare ne a tsare mutanen, ba tare da sanin yaushe za a sake su ba, hade da ajiye su a wurare marasa kyau.

Kamar yadda wani rahoto da Cibiyar Dake Yaki da ayyukan ta’addanci ta fitar ke nunawa, kungiyar ta Boko Haram ta tura ‘yan kunar bakin wake 434 a tsakanin watan Afrilun shekarar 2011 da watan Yunin wannan shekara.

Kashi 56 cikin 100, mata ne, sannan kashi 19 cikin 100 yara ne kanana ko kuma matasa.

Shirin sauya tunanin mayakan na Boko Haram, ya zama kwakwarar hanyar da gwamnatin Najeriya ke amfani da shi, domin kawo karshen hare-haren da kungiyar ke kai wa.

A bara, shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nuna kwarin gwiwa a babban taron Majalisar Dinkin Duniya inda ya ce shirin yana tasiri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG