Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ingila Ta Yanki Tikitin Haduwa Da Najeriya Bayan Doke China Da Ci 6-1


'Yan wasan Ingila bayan da suka doke China da ci 6-1
'Yan wasan Ingila bayan da suka doke China da ci 6-1

Ita dai Ingila ta lashe wasannin uku a jere ba tare da ta shan kaye ba, yayin da ita kuma Najeriya ta yi canjaras sau biyu ta kuma shammaci Australia da ci 3-2.

‘Yan wasan Ingila a gasar cin duniya ta mata da ake yi a Australia tare da hadin gwiwar New Zealand za su hada hanya da tawagar Najeriya a ranar Litinin mai zuwa a zagayen ‘yan 16.

Ingila ta doke China da 6-1 wasan da suka buga a ranar Talata yayin da a ranar Litinin Najeriya ta tashi canjaras da Jamhuriyar Ireland a haduwar da suka yi.

Ita dai Ingila ta lashe wasannin uku a jere ba tare da ta shan kaye ba, yayin da ita kuma Najeriya ta yi canjaras sau biyu ta kuma shammaci Australia da ci 3-2.

Zagayen na ‘yan 16 zai zamanto na kwaf daya ne, wato duk wanda aka yi a nasara akansa, zai fice daga gasar.

Najeriya ita ce kasar da ta fara tsallakawa zagayen na ‘yan 16 yayin da take mataki na 40 a iya taka leda a duniya a fagen wasan kwallon kafar mata bisa kididdigar FIFA.

Ingila ita ce ta hudu a duniya a iya taka leda a fannin kwallon kafar mata.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG