Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KOFIN DUNIYA NA MATA: Netherlands Ta Ci Portugal 1-0


KOFIN DUNIYA NA MATA: Netherlands da Portugal
KOFIN DUNIYA NA MATA: Netherlands da Portugal

Kasar Netherlands ta fara wasan rukunin E da yin nasara da ci 1-0 a kan kasar Portugal a gasar cin kofin duniya ta mata da aka buga a filin wasa na Dunedin a yau Lahadi, kuma Stefanie Van der Gragt ce ta ci kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci na wasan bayan bitar na’urar VAR.

‘Yan wasan Dutch sun doke Portugal da ci 3-2 shekara daya da ta wuce a gasar ci kofin nahiyar Turai a matakin rukuni, amma a wannan karon bangaren na Iberian ba su taka leda sosai ba a karawarsu da Netherlands da aka san ta da riga launin lemo kuma ba ta samu damar kai hari ba har sai minti na 82.

‘Yan wasan Dutch sun zura kwallo a daidai minti 13 daga bugun kwana, lokacin da Van der Gragt ta zura kwallo da kai a raga, amma mai taimakawa alkali ta daga tuta kan satar gida yayin da take tunanin Jill Roord ta yiwa mai tsaron raga tsaiko.

'Yar bayan Netherlands #03 Stefanie van der Gragt ta ke murna bayan tashi daga wasansu da Portugal
'Yar bayan Netherlands #03 Stefanie van der Gragt ta ke murna bayan tashi daga wasansu da Portugal

Sai dai an sauya hukuncin satar gida da aka yanke na yin katsalandan a wasan, bayan bitar VAR da alkaliyar wasan ta yi bayan ta sake kallon na’urar kuma ta bayar da kwallon, lamarin da ya haifar da murna ta biyu daga ‘yan wasan Dutch.

Van der Gragt ta shaidawa manema labarai bayan da aka bayyanata ‘yar wasan da tafi taka leda a wasan cewa “mun yi murnar zura kwallo a raga sannan kuma mataimakiyar alkaliyar ta daga tuta, don haka muka jira hukunci na karshe.”

“Ko yaushe yana da wahala ka yi murna karo na biyu amma yana da kyau. Na yi farin ciki sosai da muka yi nasara, wannan shi ne abu mafi muhimmanci a yau.”

Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG