Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IRAN: Ana Gaf da Cimma Daidaito Kan Shirin Nukiliya


Wakilan kasashen dake tattaunawa akan shirin nukiliyar Iran

Bayan sun kwashe watanni goma sha takwas suna tattaunawa akan shirin nukiliyar Iran da alamu aski ya kawo bagan goshi tare da kyautata zaton zasu cimma matsaya yau Litinin

A yau Litinin, masu tattaunawa a bangaren Iran da wakilan manyan kasashen duniya ciki har da na Amurka sun dukufa wajen ganin an kammala ganawar watanni 18 da aka kwashe ana yi domin cimma matsaya kan takaddamar nukiliyar Iran.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce yana da yakinin za a cimma matsaya guda, ko da ike, ya ce akwai batutuwa da suka rage, kuma ba zai yi alkwarin za a cimma yarjejeniya a karshen yau Litinin ba.

A jiya Lahadi, mahalarta taron suka kyan-kyasa cewa bangarorin biyu suna daf da cimma matsaya.

Yau 13 ga watan Yuli, na daga cikin jerin ranakun da bangarorin biyu suka shatawa kansu a matsayin wa’adin karshe na kulla yarjejeniya.

Sai dai, wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran, Alireza Miryousefi, ya ce babu batun ko za a kara tsawaita wa’adin.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG