Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Da Turkiya Sun Amince Da Shawarar Rasha


Jiya aka kaddamar da yarjejeniyar tudun mun tsira a Syria

Ma’aikatar tsaron Amirka tace tana maraba da duk wani yunkurin kasa da kasa na rage tarzoma domin a samu zarafin kai kayayyakin agaji na jin kai ga wadanda suke bukata a kasar Syria, sa’anan kuma daga bisani a samu hanyoyin magance rikicin kasar a siyasance.

Jiya Juma’a da tsakar dare aka kaddamar da amfani da yarjejeniyar da aka kula na samar da yankunan da ba za’a fafata a cikinsu ba.

Wakilan kasashe uku da zasu tabbatar ana mutunta yarjejeniyar, Rasha da Turkiya da kuma Syria ne suka rattaba hannu akan yarjejeniyar a karshen zagaye na baya bayan na shawarwarin samun zaman lafiya da aka yi a Astana, baban birnin kasar Kazakhstan.

A ranar Alhamis kasashen na Rasha da Turkiya da kuma Iran suka yi na’am da shawarar da Rasha ta gabatar na

samar da wadannan yankunan a cikin Syria da nufin kawo karshen rikicin da aka yi shekaru shidda ana yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG