A hukumance kasar Iran ta ayyana yau Talata a matsayin ranar zaman makokin mutanen da girgizar kasar ranar Lahadi ta rutsa dasu a yanki mai tsanukan na kan iyakar kasar da Iraq daga yammaci.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.3 akan ma’aunin girgizar kasa da kuma wasu hucinta sun kashe sama da mutane 400 da raunata wasu 7,000.Su kuma Jami’an Iraqi sun bada rahotan akalla mutuwar mutane bakwai.
Kungiyoyin masu aikin ceto a kan iyakar Iran da Iraqi na amfani da hannayensu wajen tono baraguzan gidaje, da kuma amfani da karnukan dake sunsuno mutanen da gine-gine suka danne.
Facebook Forum