Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Kai Karar Amurka Kotun Duniya


Hasan Rouhani, shugaban kasar Iran
Hasan Rouhani, shugaban kasar Iran

Biyo bayan takunkumin da Amurka ta sake kakabawa Iran wanda ya fara tasiri a harkokin tattalin arzikinta, kasar ta kai Amurka kara a kotun duniya inda ta bukaci a soke takunkumin

Gwamnatin kasar Iran ta gayawa kotun duniya jiya littini cewa sake sawa kasar Takunkumi da Amurka tayi zai durkusar da tattalin arzikin kasar kana ya jefa ilahirin yankin gabas ta tsakiya cikin mawuyacin hali. Daga nan ta roki kotun duniyar karkashin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta dakatar da matsin lambar tattalin arzikin da hukumomin dake Amurka suke yiwa I ran.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa dangane da wannan karar a gaban kotun dake birnin Hugue, Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Ponpeo ya bayyana matsayin Iran a zaman maras tushe, kana ya kare wannan matakin da Amurka ta dauka a zaman kariya ga kasar.

Amurka wacce ta ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar, a yau Talata za ta gabatar da martaninta.

A cikin watan Yuni ne dai Iran ta shigar da karar, bayan da gwamnatin shugaba Trump ta janye Amurka daga yarjejeniyar da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya kan shirin Nukiliyarta.

Wasu kawayen Amurka a Turai suna adawa da kudurin sake kakabawa Iran takunkumin domin suna ganin Iran na ci gaba da mutunta yarjejeniyar.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG