Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Zargi Amurka Da Kokarin Karya Tattalin Arzikinta Da Sauyin Gwamnati


Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jayad Zarif yana zargin Amurka da yunkurin karya kasar Iran da kuma kokarin hambarar da gwamnati ta hanyar lalata kasuwancin man ta ta kasa da kasa.

Zarif ya fada a wata hira da ya yi da shirin labaran Fox News ta nan Amurka a jiya Lahadi, ya kira wasu shugabannin duniya da kungiyar “B Team” da suka hada da firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da mai bada shawara a kan tsaroa Amurka John Bolton da shugabanni a Saudi Arabia da Hadaddiyar Daular Larabawa cewa suna iza shugaban Amurka Donal Trump zuwa ga wata gwagwarmaya da baya so.

Suna neman iza Amurka zuwa yaki inji Zarif ya kuma ce manufa ita ce daga karshe a sauya gwamnati a Iran.

Bolton ya bayyana a kan wannan shirin labaran Fox News, yana mai cewa ba manufar Amurka ce sauyin gwamnati ba, sai dai sauyin halaye, musamman kawo karshen shirinb kera makaman nukiliyar da kuma gwajin makaman ballistic.

Mutanen Iran sun cancanci gwamnati ta kwarai inji Bolton.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG