Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Tace Ba Zata Mutunta Wata Sabuwar Yarjejeniya Ba


Mideast Iran Russia
Mideast Iran Russia

Gwamnatin kasar Iran tace ba zata mutunta wani sabon yarjejeniya ba, sabanin wanda aka cimmawa da ita da Amurka dama sauran Manyan kasashen duniya.

Gwamnatin kasar Iran ta ta gargadi Amurka cewa yarjejeniyar data kulla da ita dama sauran manyan kaashen duniya ba abu ne da za ayi wani sauyi ba.

A cikin wata sanarwan da Maaikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta fitar, tace ba zata yarda da kowane irrin canji ba daga yarjejeniyar farko da aka cimmawa

Tace don haka ba wani abu da zatayi yanzu ko an jima game da wanda takeyi yanzu.

Ministan harkokin wajen kasar Mohammed Javad Zarif ya fada a shafin san a twitter cewa bayanin da shugaba Trump yayi a ranar jumaa cewa wai a shirye yake da ya kara fitar da wani sabon takumkunmi, wannan wani yunkuri ne na kawo wa yarjejeniyar da cimmawa cikas.

Sai dai wannan kalaman shugaba Trump shine irin san a ukku na ganin ansa wa kasar ta Iran takunkumi mai tsaurin gaske domin hakan yasa ta jingine batun binciken da takeyi game da shirin ta makamin ta na nukiliya.

Trump dai yace wannan ne karo na karshe da zai jingine maganar har na tsawo kwanaki 120 domin hakan ya baiwa majilisar dokokin kasar ta Amurka da sauran kawayen ta na Turai su inganta wannan batun ko kuma Amurka tayi gaban kanta na jingine yarjejeniyar ma dungurungun.

Fadar White House tace daga yanzu duk wata sabuwar yarjejeniya da kasar Iran zai hada da batunmakamin ta mai linzami.

Amma idan ba haka to Amurka ba zata yi ko wane sassauci ba ga sharuddan takunkunmin game da wannan batu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG