Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS Na Kokarin Kafa Sansanin Shakatawa a Afghanistan - Rasha


Wani yanki a kasar Afghanistan

Akwai alamun kungiyar ISIS wacce ake wa lakabi da Daesh a yankin Gabas ta Tsakiya na hada sansani a Afghanistan.

Rasha ta yi gargadin cewa kungiyar ISIS na neman ta maida yankin Arewacin Afghanistan wani wajen “hutawar” 'yan tsagerun kasa da kasa.

Jakadan Rasha a Pakistan Alexy Dedov ne ya bayyana cewar, Reshen kungiyar Da’esh na kasa da kasa ne ya dauki dawainiyar kokarin watsa 'yan ta’adda a iyakar Syria da Iraqi hade da zirga zirgarsu a fadin duniya.

Sai dai Jakadan bai fadada bayanin nasa ba duk da cewa Rasha da Iran sun jima suna zargin Amurka da goyon bayan farfadowar ISIS a Afghanistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG